1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta gargadi matan da ba sanya hijabi

April 2, 2023

Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya ce sanya hijabi doka ce da ya kamata kowacce mace ta martaba a fadin kasar gaba daya.

https://p.dw.com/p/4PbC4
Hoto: Iranian Presidency Office/APAimages/IMAGO

Shugaban na mayar da martani ne ga wani faifan bidiyo da ake yadawa wanda a cikinsa aka ga wani matashi na cin zarafin wasu mata guda biyu ta hanyar watsa musu madarar Yoghurt a fuska bisa zargin su da rashin sanya hijabi.

Raisi ya ce duk da cewa kowa na da damar fadin albarkacin bakinsa amma ya kamata jama'a su sani cewa sanya hijabi yanzu a kasar Iran doka ne. Sai dai duk da haka hukumomi a Tehran sun ce sun bayar da umurnin a kamo mutumin da ya ci zarafin matan.

A watan Satumba na shekarar da ta gabata mutuwar da matashiya Mahsa Amini ta yi a hannun 'yan Hisbah na kasar bayan kamun da suka yi mata bisa zargin ta da yin shigar da ba ta dace ba, ya haifar da zazzafar zanga-zanga wacce daga bisani ta zama sanadin mutuwar mutane sama da 500.