1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta jaddada hadin kai da kasashen Rasha da Siriya

Mohammad Nasiru Awal
April 10, 2017

Gwamnatin Iran ta ce harin da Amirka ta kai a Siriya ya nuna gazawarta a filin daga, kuma harin ya dagula tattaunawar samar da zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/2azjM
Russland Treffen Hassan Rohani mit Putin in Moskau
Hoto: Reuters/S. Karpukhin

Shugaban Iran Hassan Rouhani a wannan Litinin ya ce sun tattauna ta wayar tarfo da Shugaban Rasha Vladimir Putin inda suka sake sabunta goyon bayansu ga gwamnatin Siriya, yana mai cewa harin makamai masu linzami da Amirka ta kai a makon da ya gabata ya take 'yancin Siriya na zama kasa mai cikakken 'yancin kai. Ya fada wa wani taron manema labarai cewa harin da Amirka ta kai ya nuna gazawarta a filin daga, kuma harin ya dagula tattaunawar samar da zaman lafiya.

"Na tattauna da Mr. Putin, kuma burinmu shi ne samar da wani yanayi a Siriya da zai ba wa kungiyoyi daban-daban damar cimma yarjejeniya ta hanyar tattaunawa, za mu kuma ci gaba da yaki da 'yan ta'adda irinsu IS da Al-Nusra Front."

Iran dai ta yi kira da a kafa wani kwamitin kasa da kasa da zai gudanar da bincike na harin makaman masu linzami da kuma harin gas mai guba da ya kashe mutane da dama a Siriya, lamarin da ya janyo martanin da Amirkar ta mayar.