1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta kai ƙaran Amurika gaban komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia

May 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buzw

A dangane da badaƙallar rikici makaman nukleayar Iran, yau ne hukumominTeheran, su ka rubuta wasiƙa zuwa ga Sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia, Koffi Annan.

A cikin wasiƙar, jikadan Iran a Majalisar Ɗinkin Dunia,ya kai ƙaran Amurika, a dangane da barazanar da ta ke, ta kai famarkin sojan ga ƙasar Iran.

Iran ta buƙaci komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya tsawata wa Amurika, kasancewar wannan barazana ta saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa.

A nata gefe, gwamnatin Amurika, na ci gaba da shelar warware wannan rikici, ta hanyar diplomatia, duk da cewa, ba ta keɓe yiwuwar kai harin soja ba, ga ƙasar Iran, idan buƙatar hakan ta taso.