Iran ta kai hari kan sojin Amirka a Iraki
January 8, 2020Kwanaki biyar bayan da Amirka ta halaka Janar Qassem Soleimani, kasar Iran ta mayar da martani a wannan Laraba ta hanyar harba wasu makamai masu linzzami kimanin 15 kan wasu cibiyoyin sojin Iraki guda biyu wadanda sojojin Amirka ke girke a cikinsu.
Ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta tabbatar da afkuwar harin makaman masu linzami wadanda ta ce Iran din ta harbo su ne daga sansanonin sojinta na Ain al- Assad da kuma Erbil.Tuni dai kasar ta Iran ta fito fili ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare wadanda ke bude wani sabon babi na rikicin da ke gudana tsakanin kasar ta Iran da Amirka.
Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya ce barnar da hare-haren suka yi ba ta taka kara ta karya ba.
Yanzu haka dai hukumar kula da harkokin jiragen sama ta kasar Amirka ta haramta wa jiragen sama kasar ta Amirka masu jigilar fasinja, ratsawa ta sararin samaniyar kasashen Iran da iraki da ma sauran kasashe na yankin Golf baki daya.