Iran ta kai karar Kanada gaban kotu ICJ
June 28, 2023Talla
Kasar Iran ta kalubalanci gwamnatin Ottawa da sanya sunanta cikin wadanda suka dauki nauyin 'yan ta'adda a shekarar 2012, a lokacin da Kanada ta yanke alakar diflomasiyya da kasar tare da rufe offishin jakadancinta da ke Tehran baya ga korar jami'an diflomasiyar Iran daga kasar.
Iran ta ce, Kanada ta take dokar kasa da kasa na hukuncin kotu da ya bai wa Iran umurnin mika wasu kadarori ga wadanda harin kungiyoyin da Tehran din ta dauki nauyi ya shafa. Sai dai har yanzu kasar Kanadar ba ta mayar da martani kan matakin na Iran ba.