Iran ta kakaba wa 'yan Turai takunkumi
October 26, 2022Wasu 'yan majalisar dokokin Faransa da kuma manaima labarai biyu na jaridar Bild ta Jamus na daga cikin wadanda gwamnatin Iran ta sanya wa takunkumi. A cikin sanarwar da ta fitar a birnin Teheran, ma'aikatar harkokin wajen Iran ta zarge su da goyon bayan 'yan ta'adda tare da haddasa tashin hankali a kasar.
Takunkumin ya hada da haramta musu biza da kuma kwace dukiyoyi da kadarorinsu a yankin da ke karkashin ikon Iran. Wannan mataki ya zo ne mako guda bayan da Iran ta fara sanya takunkumi kan wasu jami'ai da hukumomin Birtaniya, bayan da Landan ta kakaba wa 'yan sandan da'a na Iran takunkumi saboda mutuwar Mahsa Amini.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dubban mutane suka taru a kabarin matashiya Mahsa Amini a yankin Kurdistan domin yi mata adu'o'i na karshen makokin kwanaki 40 da aka saba a Iran.