Iran ta ce za ta koma inganta uranium
July 7, 2019Wannan matakin na Iran dai na zuwa ne bayan da wa'adin da shugaban kasar Hassan Rohani ya debarwa kasashen Turai na su fitar da kasar daga matsin tattalin arziki bayan sababbin takunkuman Amirka, ko kuma su dakatar da mutunta wasu sassa na yarjejeniyar ya cika ba tare da daukar matakan daga kasashen Turan ba.
Kakakin hukumar makamashin nukilya ta kasar ta Iran Behrouz Kamalvandi ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai, inda ya ce idan Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya ta zo auna karfin uranium din kasar to za ta taras ya zarce wanda aka takaita mata a yarjejeniyar ta 2015
Kasar ta Iran dai ta jaddada cewa shirin nata na zaman lafiya ne dan wadatar da kasar da makamashi ba dan kera makamin nukiliya ba, dan haka tana bukatar sarrafa uranium din nata har zuwa kaso biyar cikin 100 domin amfani da shi a tashar nukiliyar makamashin Bouchehr da ke a Kudu maso Arewacin kasar.