Iran ta lashi takobin ci gaba da atisayin soji a mashin ruwan Hormuz
December 30, 2011Ta gwada makamanta masu linzami ne dai kasar Iran za ta tabbatar da baraznar da ta yi cewa zata toshe mashigin ruwan Hormuz da ke da muhimmavi ga aikin dakon man fetur a duniya. Shugabannin sojin kasar sun ce a matsayin matakin karshe na atisayin da suka shafe kwanaki tana gudanarwa a tekun Gulf, ta shirya gwada makamai masu linazami a ranar Asabar 31-12-2011 cikinsu har da mai iya kaiwa zango mai nesa. A 'yan kwanakin nan ne Iran ta yi barazanar toshe mashigin ruwa da ke tsakanin tekun Gulf da tekun Arabia in har kasashen yamma suka aza mata haramcin sayar da man futurta a kasuwannin duniya bisa takaddamar da ake yi akan shirinta na nukiliya.
Amirka ta gargadi shugabannin Iran da kakkausan harshe game da wannan aniya tata. Rundunar ruwan Amirka ta ce sam ba zata sa ido ta ga an kawo cikas ga zirga zirga jiragen ruwa a wannan yanki ba tana mai nuni da sojojin da ta girke a yankin. Ta wannan mashigi mai fadin kilomita 50 ne dai ake bi da kashi 40 daga cikin dari na man fetur da ake bukata a duniya.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal