1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta maida martani ga tayin Amurika na shiga tantanawar rikicin makaman nuklea

June 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buvn

Ƙasar Iran ta maida martani ga saban tayin da Amurika ta yi mata, na watsi da shirin ƙera makaman nukleya.

Ministan harakokin wajen Iran, Manoucher Mottaki, ya hurta cewa, kasar sa, zata ci gaba, da sarrapa Uranium, da zumar ƙarfafa makamashin nukleya, amma kuma a ɗaya hannun, a shire ta ke, ta hau tebrin shawara.

Wannan kalamomi, sun biwo bayan hurucin sakatariyar harakokin wajen Amurika, Condoleesa Rice, inda ta bayyana saban matsayin gwamnatin Amurika a kan wannan batu.

Ta ce a yanzu, Amurika a shire ta ke, ta haɗu da sauran ƙasashe domin yin tantanawar ƙeƙe da ƙeƙe da hukumomin Iran.

A halin da ake ci dai, ƙasashen dunia, na ci gaba da yin lalle marhabin da wannan saban mataki, da Amurika ta ɗauka.

Ƙasashen Rasha da China, da ke bada goyan baya ga Iran, sun ce hakan, babban ci gaba ne, a faɗi ka tashin warware taƙƙadamar nuklea.

Nan gaba a yau ne ake sa ran ministocin harakokin wajen kasashen masu kujerun dindindin a Majalisar Dinkin Dunia, gami da Jamus,za su gabatar da wata sabuwar shawara ta fita daga wannan baddaƙala.