1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta musanta batun tattaunawa da Trump

Abdoulaye Mamane Amadou
September 26, 2019

Shugaba Iran Hassan Rohani ya musanta jita-jitar da kae yadawa cewar akwai yiwuwar ya gana da takwaransa na Amirka Donald Trump a yayin taron koli na Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana yanzu haka a birnin New York.

https://p.dw.com/p/3QGX5
USA Hassan Rohani spricht vor der UN-Vollversammlung
Hoto: AFP/D. Angerer

Shugaba Rouhani ya ce duk wata tattaunawa ba za ta yiwu ba muddin Amirka ta ci gaba da kafewa a matsayinta na kakaba takunkumai na kariyar tattalin arziki ga Iran, shugaban ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da jawabinbsa a zauren na Majalisar Dinkin Duniya.

Rahotanni sun ce matsayin da shugaban Iran Hassan Rouhani ya bayyana, ya kara yin fatali da duk wani yunkurin da wasu manyan kasashen duniya suke da shi na sulhunta rikicin da ya kara daukar dimi tsakanin Amirka da Iran, tun bayan kaddamar da wani hari kan matatun man fetir din kasar Saudiyya a tsakiyar wannan watan, harin da kuma Saudiyya da Amirka suka nuna 'yar yatsa ga Iran da cewa ita ce ta ke da alhakin kai harin.