1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Iran ya bukaci kawo karshen rikicin Yemen

Suleiman Babayo
September 25, 2019

Lokacin jawabi a gaban zauren taron Majalisar Dinkin Duniya Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya bukaci kasar Saudiyya ta kawo karshen yakin da ke faruwa a kasar Yemen.

https://p.dw.com/p/3QFu7
USA Hassan Rohani spricht vor der UN-Vollversammlung
Hoto: Reuters/C. Allegri

Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya bukaci kasar Saudiyya ta kawo karshen yakin da ke faruwa a kasar Yemen bayan harin da aka kai kan wuraren hakar man fetur na Saudiyya da Amirka ke zargi Iran da hannu.

Lokacin da yake jawabi a taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya, Shugaba Rouhani ya ce Saudiyya take da tabbaci na iya kawo karshen yakin na Yemen, inda 'yan tawayen Houth da ke samun goyon bayan Iran ke fafatawa da kawancen sojoji da Saudiyya ke jagoranci.

Kana Shugaban na Iran ya ce kasar ba za ta sake tattauna batun nikiyar kasar ba muddun tana karkashin takunkumin karya tattalin arziki.