1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta nemi rance gaggawa daga Asusun IMF

Mohammad Nasiru Awal USU
April 8, 2020

Iran kasar da ke cikin kasashen da Coronavirus ta fi yin kamari, ta yi kira ga Asusun IMF da ya bata bashin gaggawa don yakar cutar da ta zama annoba a duniya.

https://p.dw.com/p/3aeCO
Iran Ghom | Coronavirus | Haschd asch-Schabi, Desinfektion durch Milizen
Hoto: Fars

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya yi kira ga Asusun Bada Lamuni na Duniya, IMF, da ya ba wa kasarsa mai fama da annobar Corona, bashin gaggawa na dala miliyan dubu 5 don yaki da cutar.

Kasar ta Iran dai na a jerin kasashen duniya da suka fi jin jiki sakamakon Covid-19, da yanzu ta ce ta yi sanadin rayukan mutane kusan 4,000 a kasar sannan fiye da mutum dubu 64 da 500 sun harbu da kwayar cutar. Sai dai akwai jita-jita a duniya cewa yawan wadanda cuta ta yi ajalinsu da wadanda suka harbu da ita ya zarta adadin da mahukuntan Iran din suka bayar.

Iran dai ta ce tana bukatar abin da zai iya zama bashin farko daga IMF cikin shekaru fiye da 50 don ta ci gaba da yakar cutar Corona. Sai dai rahotanni sun ce kasar Amirka da ke zama babbar abokiyar gabatar Iran, da kuma ke da ikon hawa kujerar naki a IMF, za ta hana ba da rancen, bisa zargin cewa Iran za ta yi amfani da su a fannin aikin sojinta.