An rataye mai adawa da gwamnatin Iran
December 12, 2022Mahukuntan kasar Iran sun sake aiwatar da hukuncin kisa kan daya daga cikin masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar da ya jima a tsare.
An aiwatar da hukuncin kisan kan Majidreza Rahnavard ne bayan da kotu ta same shi da laifin hannu a kisan wasu jami'ai biyu na rundunar nan ta Basij da ta yi kaurin suna wajen amfani da karfi yayin kwantar da tarzoma a kasar.
A makon da ya gabata ma dai, mahukuntan na Tehran sun bayar da umarnin rataye wani mai zanga-zanga Mohsen Shekari bisa laifin jikkata wani jami'in tsaro a yayin zanga-zangar.
Yazuwa yanzu, an kiyasta cewa masu zanga-zanga sama da dubu goma sha biyar aka kama, inda aka gurfanar da mutum dubu biyu tare da yanke musu hukuncin kisa a hukumance.
Iran ta fada cikin rudani, tun bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini da ake zargin ta mutu saboda azabar da jami'an Hisbah suka gallaza mata bisa laifin kin mutunta dokar sanya hijabi.