1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rushe hukumar da ke tabbatar da saka Hijabi a Iran

December 4, 2022

Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a kasra Iran masu boren sun shirya gudanar da gangami sakamakon rushe hukumar 'yan sanda gyara tarbiyya da ke tilasta mata aiki da dokar saka hijibi.

https://p.dw.com/p/4KSR6
Iran I Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Iran
Masu zanga-zanga a IranHoto: SalamPix/abaca/picture alliance

A wannan Lahadin, masu zanga-zanga a Iran sun bukaci 'yan kasar da su shiga yajin aikin kwanaki uku a wani mataki na matsin lamba ga hukumomin kasar bayan sanarwar rushe hukumar Hisban kasar.

A wani mataki na tsayawa kan bakarsu ta adawa da gwamnatin kasar, masu boren sun kuma shirya gudanar da taron gangami a ranar Laraba mai zuwa a birnin Tehran fadar gwamnatin kasar. Kawo yanzu dai hukumomin Tehran ba su yi wani karin bayani ba tun bayan fitar da sanarwar rushe hukumar da ake ganin za ta yi tasiri wajen kwantar da hankula a kasar. Yayin da wasu kungiyoyi a kasar ke ganin soke dokar tilasta sanya hijabi ce kadai za ta magance rikicin da kasar ta fada, jami'ai a kasar sun jadadda cewa gwamnatin Tehran ba za ta soke dokar da ta shinfida bisa dokokin addinin Musulunci ba.

Kasar Iran dai ta fada cikin rikici, tun bayan mutuwar matashiyar nan Mahsa Amini a hannun jami'an 'yan sandan gyara halinka na hukumar sakamakon karya dokar da ta yi, lamarin ya haifar da zanga-zanga da ke rikidewa zuwa tarzoma wanda ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane.