Iran ta sake yi wa Amirka barazana
January 2, 2021Babban kwamandan mayakan juyin juya hali na kasar Iran Janar Hossein Salami, ya ce shirye kasar take domin mayar da martani a kan karfin soja da Amirka ke yi wa kasar, duk da zafafa kalamai da Shugaba Trump wanda wa'adinsa ke zuwa karshe yake yi.
Janar Hossein Salami, na magana ne a wani biki da aka yi a jami'ar birnin Tehran, bikin da aka yi domin tunawa da kisan kwamadan yakin kasar, Janar Qassem Soleimani, da Amirka ta yi a farkon watan Janairun bara a Iraki.
A lokacin ma dai Iran din ta kai harin ramuwar gayya da makamin mai linzami a sansanin sojan Amirka da ke Irakin, inda akalla wasu sojojin Amirkar 100 suka sami matsala ta kwakwalwa da sauran munanan raunuka.
A cikin kalamansa a lokacin taron na jami'ar Tehran, kwamandan mayakan na Iran, Janar Hossein Salami, ya ce Iran ba ta da wata matsala ko taraddadin iya mayar wa da Amirka kowane irin martani.