1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Karuwar sinadarin uranium

Binta Aliyu Zurmi
November 23, 2022

Mahukunta a Iran sun sanar da cewar ya zuwa yanzu sun kai kaso 60 cikin dari a kokarin samar da sinadarin uranium din su a tashar Fordo da ke karkashin kasa.

https://p.dw.com/p/4Jvft
Atomanlage im Iran
Hoto: Getty Images

Tehran ta ce shekaru uku ke nan da suka fara wannan aiki tun bayan da aka wargaza yarjejeniyar makamashin nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 tsakaninta da manyan kasashen duniya.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Kasa da Kasa IAEA da kasashen yamma ke zargin Iran da mallakar sinadarin da ya wuce kima 

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliyar kasar Iran Mohammad Eslami, ya ce matsi da kuma takunkumai ba su ne za su magance matsalar ba.

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma a shekarun baya, ba a amince Iran ta sami sinadarin da yawanshi ya kai kaso 4 cikin dari ba wanda ake ganin ya isa duk wata bukata baya ga kera makaman nukiliya.