1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta soma kwance tashonshin nukliyarta

Gazali Abdou tasawaNovember 2, 2015

Iran ta soma aiwatar da matakin kwance shirinta na nukliya kamar yadda yarjejeniyar da ta cimma da manyan kasashen duniya a ranar 14 ga watan Yulin wannan shekara ta tanada.

https://p.dw.com/p/1GyMA
Iran Atomfabrik Fordo bei Ghom
Hoto: picture-alliance/dpa

Kasar Iran ta bada sanarwar soma aiwatar da matakin kwance shirin nukliyarta wanda yarjejeniyar da kasar ta cimma da manyan kasashen duniya ranar 14 ga watan Yulin wannan shekara ta tanada. Shugaban hukumar makamashin nukiliyar kasar ta Iran Akbar Salehi ne ya sanar da hakan a wannan Litinin a kasar Japan inda yake gudanar da wata ziyarar aiki.

Daga cikin matakan kwance shirin nukliyar da kasar ta Iran ta fara aiwatarwa sun hada da soma kwance na'urorin cibiyoyin tsuma sinadarin Uranium na Nantanz da Fordow. Sai dai kamfanin dillancin labaran kasar ta Iran na FARS ya ruwaito cewa wasu manyan mutane 20 daga cikin masu ra'ayin rikau na kasar ta Iran sun rubuta wasika zuwa ga Shugaba Hassan Rohani domin nuna adawarsu da wannan mataki.