Iran ta toshe shafin Google a ƙasar
September 24, 2012Har wa yau mahukuntan na Tehran sun ce ƙasar za ta ƙauracewa bikin bada kyauta na Oscars ga wanda su ka yi bajinta wajen shirye fina-fianai a shekara mai zuwa muddin masu shirya gasar ba su yi Allah wadai da fim ɗin nan da ya ci zarafin Musulunci ba.
Da ya ke jawabi ga kamafanin dillancin labarai na Mehr, wani mai magana da yawun gwamnatin ta Iran ya ce ɗaukar wannan matakin ya zama dole bayan da galibin al'ummar ƙasar su ka buƙaci Tehran ɗin ta yi hakan.
A tasa zantawar da manema labarai ministan da ke kula da harkokin al'adu na ƙasar Javad Shamgadri cewa ya yi mahukuntan ƙasar ba su da wani zaɓi da ya wuce rungumar buƙatun jama'arsu kuma dole ne su nuna fushinsu kasancewa an yi karen tsaye ga addininsu da ke da mabiya kimanin biliyan ɗaya da rabi a faɗin duniya.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh