Iran ta yake hukunci akan wasu Amirkawa biyu
August 20, 2011Talla
Tashar tebebijin ta kƙasar Iran ta bayyana cewa kotun ƙasar ta sami wasu Amirkawa biyu da aka kama shekaru biyun da suka gabata da laifin leƙen asiri da kuma shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba. Su dai Shane Bauer da kuma Josh Fattal waɗanda ke da shekaru 28 da haihuwa ko wannensu, ya ƙi ya amsa laifukan da aka zarge su da aikatawa a inda suka ce sun kutsa ƙasar ne bisa kuskure saboda rashin shinge da ke nuna iyaka a lokacin da suka yawace yawace a lardin Kurdistan da ke arewacin ƙasar Iraki. Tashar telebijin ɗin ta ƙasar Iran ta ce an yanke wa Amirkawan biyu hukuncin ɗaurin shekaru takwas a gidan yari.
Mawallafi: Mouhmadou Awal Balarabe
Edita: Halima Balaraba Abbas