Iran ta yi tir da harin Amurka da Burtaniya suka kai Yemen
February 25, 2024Kasar Iran ta yi allawadai da hare-haren da Amurka da Burtaniya suka kai Yemen, inda ta ce wannan kokarin haddasa rincabewar rikicin ne kawai a yankin.
Karin bayani:Amirka ta lalata makaman 'yan Houthi a tekun Bahar Maliya
Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kanani ya fitar a Lahadin nan, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito, yana mai kokawa da yadda manyan kasashen biyu suka gaza yin katabus wajen dakatar da yakin Gaza.
Karin bayani:Amurka da Burtaniya sun kai sabbin hare-hare Yemen
Tun bayan fara yakin Gaza ne 'yan tawayen Houthi suka fara kai hari kan jiragen ruwan da ke bi ta Baharmaliya, a matsayin martani ga yakin, inda mai magana da yawunta Yahya Saree ke ba da tabbacin ci gaba da ka wa jiragen farmaki har sai an dakatar da yakin Gaza.