Iran ta yi barazanar sake kera makamashin nukiliya
April 22, 2018Ministan harkokin wajen kasar Javad Zariff ne ya sanar da hakan inda ya ce da zarar Amirka ta karya dokokin yarjejeniyar, Iran ba za ta jinkirta daukar matakin mayar da martani ba. An cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran bayan da aka shafe tsawon lokaci ana tattaunawa a tsakanin manyan kasashen duniya shida, a karkashin yarjejeniya, kasar ta Iran ta amince ta rage karfin yadda ta ke sarrafa sinadarin uranium inda aka yi alkawarin janye takunkumin da majalisar dinkin duniya ta garkama ma ta.
An kulla yarjejeniyar a lokacin gwamnatin Barack Obama, sai dai shugaba Donald Trump ya sha yin barazanar fitar da kasar daga shirin, sauran kasashen da aka cimma matsaya tare sun hada da Britaniya da Faransa da Rasha da Chana da kuma Jamus sai Amirkan, wadannan kasashen na ci gaba da lallamin Trump kan mutunta wannan yarjejeniyar.