Iran ta yi fatali da ƙudirin Majalisar ɗinkin duniya
August 1, 2006Iran ta yi watsi da ƙudirin Majalisar ɗinkin duniya wanda ya buƙaci dakatar da shirin ta na nukiliya nan da ƙarshen wannan watan. Shugaban ƙasar Mahmoud Ahmedinejad ya lashi takobi ƙasar sa ba zata bada kai bori ya hau ba, don wasu kalamai na tsoratarwa ko kuma tursasawa ba. Jawabin na sa ya zo ne kwana ɗaya bayan da kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya ya zartar da ƙudiri a kan Iran ɗin na dakatar da shirin nukiliyar ta nan da ƙarshen wannan watan na Augusta ko kuma ta fuskanci yiwuwar sanya mata takunkumi.
Ahmedinejad yace alúmar ƙasar Iran nada cikakken haƙƙin sarrafa makamashin nukiliya ta hanyar lumana kuma ba zasu yarda a ƙwace musu wannan damar ba. Yace Idan wasu ƙasashe na tsammanin cewa za su tsorata ƙasar da kalamai na kurari, to kuwa sun yi babban kuskure, idan kuma basu fahimci hakan ba, za kuwa su ɗanɗana kuɗar su wataran. Jakadan Iran a Majalisar ɗinkin duniya ya baiyana ƙudirin da cewa bai dace ba kuma ba zai haifar da komai ba sai ƙara dagula alámura. Kwamitin tsaron ya buƙaci shugaban hukumar majalisar ɗinkin duniya mai lura da hana yaɗuwa makaman nukiliya Mohammed el-Baradei ya baiyana mata idan Iran ta komo kan hanya.