Iran ta yi gwajin wasu makamai masu linzamin da ta inganta
December 31, 2012A wannan Litinin, hukumomin kasar Iran sun sanar da samun nasarar gwajin wasu makamai masu linzami biyu da kasar ta kara inganta su a dai dai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce game da yiwuwar kaddamar da yaki a tekun Fasha. Wani kakakin sojojin ruwan kasar ta Iran ya ce sunfurin makamai masu linzamin da za su ci matsakaitan zango, tuni kasar ta yi nasarar girka su akan manyan jiragen ruwan yakinta.
Kanfanin dillancin labaran kasar ta Iran ya kuma ruwaito cewar kasar ta inganta makamai masu linzamin da ke cin gajeren zango - sunfurin Nasr, wanda zai iya la'la'ta manyan jiragen dakon man fetur da za su iya daukar tan dubu 30, wadanda su ma ta yi nasarar gwajin na su, kuma za ta iya kaddamar da hari da su ne ko dai ta kasa ko kuma ta jiragen ruwa.
A baya bayannan dai Iran na ci gaba da gudanar da atisayen soji a dai dai lokacin da kasashen duniya ke kara nuna damuwa akan shirin nukiliyarta, wanda Isra'ila ke cewar bata kawar da yiwuwar kaddamar da hari akan cibiyoyin nukiliyar Iran din ba domin hana ta sukunin kera makaman kare dangi.
Sai dai kuma janar-janar na sojojin Iran sun na'na'ta kashedin cewar ba za su yi wata-wata ba wajen harba makamai masu linzamin da za su iya kaiwa kasar Isra'ila muddin ta kuskura ta aiwatar da barazanarta.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal