Iran ta yi kashedi ga Amurka
April 27, 2006Jagoran addini na ƙasar Iran Ayatollah Ali Khameni ya ja kunnen Amurka da cewa Ahir ta kaiwa Iran farmaki. Yana mai cewa Iran za ta ɗauki fansa tare da kai hari a kan cibiyoyin Amurka dake ko ina a faɗin duniya. Khameni yace Amurka za ta yi nadamar abin da ta aikata idan ta kuskura ta fadawa Iran da ƙarfin soji. Jawabin ya zo ne bayan da shugaban ƙasar Iran Mahmoud Ahmedinejad ya lashi takobin cewa Tehran za ta yi fatali da ƙudirin majalisar ɗinkin duniya da ya bukaci ta dakatar da ayyukan nukiliyar ƙasar. Bugu da kari Ahmedinejad ya kuma yi barazanar yanke hulɗar jakadanci da hukumar makamashin nukiliya ta majalisar ɗinkin duniya idan majalisar ta ɗinkin duniya ta ƙaƙabawa Iran din takunkumi. Kwamitin tsaron na majalisar ɗinkin duniya ya baiwa waádin nan da ranar jumaá ta dakatar da dukkan ayyuka na sarrafa sinadarin Uranium.