1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi watsi da shiga shawarwari da Amirka don warware rikicin Iraqi.

June 18, 2006
https://p.dw.com/p/ButR

Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, ya ce ƙasarsa ba za ta shiga shawarwari da Amirka ba, don warware batun rikicin Iraqi, duk da bukatar yin hakan, da wani babban jami’in siyasar Iraqin ya miƙa wa mahukuntan birnin Teheran.

A jiya asabar ne dai, Abdul Aziz al-Hakim, shugaban Kwamitin Ƙoli na Juyin Juya Halin Islama a Iraqi, wata muhimmiyar jam’iyyar ’yan shi’iti a ƙasar, wadda kuma ke da kyakyawar hulɗa da Iran, ya bayyana cewa, shawarwari kai tsaye kan wannan batun, tsakanin Iran da Amirka za su janyo fa’ida ga mahukuntan Bagadaza da na Teheran.

Amma da yake mai da martani yau, Hamid Reza Asefi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ɗin, ya ce, wannan batun bai ma taso a ajandar shugabannin ƙasarsa ba. Tun cikin watan Ifirilu da ya gabata ne shugaba Mahmoud Ahmadinejad, ya ce babu wata bukatar yin wannan shawarwarin da Amirka, saboda Iraqin na da gwamnatinta. A ɗaya ɓangaren kuma, shugaban addinin ƙasar, Ayatullah Ali Khamenei, ya ce Iran ba za ta shiga ko wane shawarwari da Amirka ba, sai Washington ta sake halin cin zalin da take yi wa Teheran.

A ce-ce ku cen da ƙasashen biyu ke yi da juna dai, Amirka na zargin Iran ne da mara wa ’yan tawayen Iraqi baya, da tallafa wa ƙungiyoyin da ke yaƙan Isra’ila da kuma yunƙurin sarrafa makaman ƙare dangi. Ita ko Iran, tana watsi ne da duk wannan zargin.