1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi watsi da takunkumi akan sayen manta

January 26, 2012

Majalisar Tehran ta yi mahawara kan kudurin haramta sayer wa nahiyar Turai Mai

https://p.dw.com/p/13rB4
Iranian President Mahmoud Ahmadinejad, speaks at a ceremony in Iran's nuclear enrichment facility in Natanz, 300 kms 186 (miles) south of capital Tehran, Iran, Monday April, 9, 2007. Iran announced Monday that it has begun enriching uranium with 3,000 centrifuges, a dramatic expansion of a nuclear program that has drawn U.N. sanctions and condemnation from the West. President Mahmoud Ahmadinejad said Monday at a ceremony at the enrichment facility at Natanz that Iran was now capable of enriching nuclear fuel "on an industrial scale." Asked if Iran has begun injecting uranium gas into 3,000 centrifuges for enrichment, top nuclear negotiator Ali Larijani replied, "Yes." He did not elaborate, but it was the first confirmation that Iran had installed the larger set of centrifuges after months of saying it intends to do so. (AP Photo/Hasan Sarbakhshian)
Mahmud AhmadinejadHoto: AP

Shugaba Mahmud Ahmadinejad na kasar Iran, ya yi watsi da shirin Turai na sanya takunkumin sayer da Mai a kan Tehran. Ya ce hakan bazai tilastawa kasarsa dakatar da shirinta na Nukiliya ba. Sai dai shugaban na Iran ya bayyana cewar a shirye gwamnatinsa take, ta zauna teburin tattaunawa da manyan kasashe masu fada aji, domin fayyace shirin Nukiliyar kasarsa. A wani abunda ke zama martanin rama wa kura aniyarta, a yau ne majalisar dokokin Iran din tayi mahawara dangane da wani kuduri dake bukatar daukar matakan gaggauta dakatar da sayar wa turai man petur. Tuni dai kasar China ta yi suka da kakkausar murya kan takunkumin tattalin da Turan ke neman kakabawa Iran, tare da cewar daukar wannan mataki na tursasawa iran bazai cimma wata manufa ba.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman