1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta zargi Amirka da haddasa mata bore

Binta Aliyu Zurmi MAB
October 3, 2022

A karon farko, Jagoran juyin juya halin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya fito ya yi jawabi ga al'ummar kasar a kan mumunar zanga-zangar da kasar ke fuskanta tun bayan mutuwar wata matashiyar a hannun jami'an Hisba.

https://p.dw.com/p/4HhGN
Ayatollah Ali Khamenei
Hoto: IRANIAN LEADER PRESS OFFICE/AA/picture alliance

Shugaban addini na Iran Khamenei ya yi amfani da wannan mataki wajen nuna jimamin mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun jami'an tsaro. Amma kuma a daya hannun ya dora alhakin rikicin da kasar ke fuskanta a yanzu haka a kan kasashen Amirka da Isra'ila.

Dama dai daruruwan dalibai na ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati, inda ko a jiya Lahadi suka yi arangama da masu goyon bayan gwamnati, lamarin da ya sa jami'an tsaro kama da dama daga cikinsu. Saboda haka ne a yau Litinin Iran ta rufe babbar jami'ar kimiyya da ke Tehran.

Sai dai a daya bangaren, da yammacin wannan rana ta Litinin kasar Kanada ta sanar da kakaba wa Iran din wasu jerin takunkumai bisa zargin ta da take hakkin bil Adama da ya kai ga mutuwar matashiya mahsa Amini.