1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta zargi Israila da hari kan nukiliyarta

April 13, 2021

Iran ta zargi Isra'ila da kai mata hari a tashar nukiliyarta da ke da matukar muhimanci a kasar.

https://p.dw.com/p/3rugd
Iran Atomprogramm
Hoto: Iranian Presidency Office/AP Photo/picture alliance

Harin da aka kai wa tashar nukiliyar Iran ta Natanz, babbar barazana ce ga tattaunarwar da ake yi kan farfado da yarjejeniyar 2015 da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran kan shirin nukiliyarta.

Iran dai ta zargi Isra'ila da kai hari kan cibiyar nukiliyar mai matukar muhimmanci. Tuni fadar gwamnatin Amirka a White house ta nisanta kanta daga harin.

A halin da ake ciki yanzu babu tabbas game da makomar yarjejeniyar duba da yadda harin ya harzuka mahukuntan na Tehran.