Iran ta zargi Majalisar Ɗinkin Duniya da munafunci.
November 13, 2006Shugaba Mahmoud Ahmadinijad na Iran, ya yi kakkausar suka ga Majalisar Ɗinkin Duniya, saboda abin da yake gani kamar rashin adalcin da take nuna wa ƙasarsa. Shugaban ya nuna ɓacin ransa ne musamman ga matakin da Majalisar ke niyyar ɗauka na sanya wa Iran takunkumi dangane da shirinta na mallakar makamashin nukiliya. Babban munafunci ne dai ganin cewa, ƙasashen da suka ja ɗamara kicinkicin da makaman nukiliya, su kuma ne ke ta ƙoƙarin hana wasu ƙasashen yin amfani da fasahar nukiliyan ta hannunka mai sanda, inji Ahmadinijad.
Shugaban na Iran, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa wani taron Ƙungiyar zaman lafiya ta majalisun ƙasashen Asiya da aka buɗe a birnin Teheran. Jawabin nasa dai ya zo ne kwana ɗaya bayan da shugaba Vladimir Putin na Rasaha ya gana da shugaban tawagar Iran kan shawarwarin makamashinn nukiliyanta, wato Ali Larijani, a birnin Moscow. Ita dai Rashan ta bukaci Iran ne da ta koma kan teburin shawarwarin ƙasa da ƙasa da ake yi kan batun makamashin nukiliyanta.
Har ila yau dai, ita Iran ɗin, na musanta zargin da Amirka ke yi mata ne, na cewa tana shirin sarrafa makaman nukiliya.