Iran ta zargi Saudiyya da Amirka kan harin Teheran
June 7, 2017Jagoran Muslunci na kasar Iran da ma babbar rundunar sojin kasar sun zargi kasashen Amirka da Saudiyya da kasancewa da hannu a cikin jerin hare-haren ta'addancin da aka kai a wannan Laraba a birnin Teheran da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 13 da raunata wasu 46.
A cikin wata sanarwa da mahukuntan kasar ta Iran suka wallafa a kamfanin dillancin labaran kasar na ISNA sun bayyana cewa hare-haren ta'addancin wadanda suka wakana kwanaki kalilan bayan ganawar da shugaban Amirka Donald Trump ya yi da abin da suka kira shugaban wata munafukar gwamnati ta yankin Golf da ta jima tana taimaka wa aiyukan ta'addanci, na cike da ma'ana.
Kuma ikirarin da kungiyar IS ta yi na daukar alhakin wadannan hare-hare na kara tabbatar da cewa Saudiyya da Amirka na da hannu a cikin lamarin. Jagoran Musluncin kasar ta Iran dai ya sha alwashin daukar fansar jinin bayin Allan da aka zubar ba da hakkinsu ba.