Iran ta kashe mutanen da ta kama da laifin cin amanar kasar
December 4, 2022A wannan Lahadin, Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan 'yan kasar da ta ce ta samu da laifin cin amanar kasar. Gwamnatimn Tehran ta tabbatar da yadda ta gano cewa, mutanen hudu, na yi wa Hukumar leken asirin Isra'ila ta Mossad aiki, suna kwarmata mata baiyanan sirrin kasar a yayin da ita kuma hukumar, ke ba su makamai da makuddan kudaden intanet na Crypto a bakacin aikin da suke yi mata.
Mutanen sun yi ta zama barazana ga tsaron kasar inda suke garkuwa da mutane suna tatsar baiyanai daga garesu, a wasu lokuta ma, suna kai hare-hare da ke lalata gine-ginen gwamnati, kamar yadda gwamnatin Tehran din ta sheda.
Wadanda aka zartas da hukuncin kisan a kansu, sun hada da Hossein Ordoukhanzadeh da Shahin Imani Mahmoudabadi da Milad Ashrafi da kuma Manouchehr Shahbandi. Isra'ila da Iran dai manyan abokan gaba ne da ba sa ga maciji da juna.