1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran tace sake kaita gaban komitin sulhu zai hana tattaunawa

July 16, 2006
https://p.dw.com/p/BuqM

Kasar Iran a yau tace sake mayarda batun nukiliyata gaban komitin sulhu zai iya zamo karan tsaye ga yiwuwar tattaunawa da ita dangane da shirinta na nukiliya.

An sake mayarda batun na Irna gaban komitin sulhu ne,bayan ta ki bada amsa dangane da tayin ihsani da kasashen turai 6 sukayi mata domin ta dakatar da shirin nata na inganta uraniyum.

Iran ta baiyana afili cewa,tana son a tattauna amma fa ba zata dakatar da inganta sinadarin uraniyum ba,sai dai jamian diplomasiya na kasashen yamma sunce mai shiga tsakani na Iran a tattaunawar Ali larijani bai nuna wata alama ta neman a ci gaba da tattaunawar ba,a lokacinda ya gana da jakadan taraiyar turai a ranar talata.

Manyan kasashen duniya dai sun amince su tattauna a mako mai zuwa game da gazawar Iran din ta bada amsa,wadda tace sai zuwa ranar 22 ga watan agusta ne zata bayar.

Yayinda kasashen Burtaniya,Faransa da Amurka da kuma Jamus suke goyon bayan kafawa Iran takunkumin karya tatalin arziki idan taki bada goyon bayanta,kasashen Sin da Rasha kuma sunce basa goyon baya.