1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran tana duba yuwuwar tura dakaru Siriya

Suleiman Babayo ATB
December 3, 2024

Siriya ta nemi taimakon Iran da sauran kasashen da suke daswa domin yaki da 'yan ta'adda inda tuni kasar Iran ta ce tana duba yuwuwar tura dakarun domin taimakon sojojin kasar Sirya yaki da 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/4nhm7
Rikicin Siriya
Rikicin SiriyaHoto: Bilal Alhammoud/Middle East Images/AFP via Getty Images

Kasar Iran ta bayyana cewa tana duba bukatar da kasar Siriya ta gabatar mata na neman dakarun da za su taimaka wajen dakilke hare-haren 'yan tawaye da gwamnatin kasar take fuskanta. Abbas Araghchi ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya ce gwamnatin ta Siriya da ke dasawa da kasarsa ta bukaci tura mata dakaru, kuma yanzu haka ana duba wannan bukata.

Karin Bayani: Faransa ta bukaci kare rayukan fararen hula a Siriya

Haka ya biyo bayan yadda wasu 'yan tawaye masu kaifin kishin addinin Islama da ke yankin arewacin Siriya suka kwace garin Aleppo birnin na biyu mafi girma a kasar daga hannun dakarun gwamnatin Siriya. Tuni gwamnatin Shugaba Bashar  al-Assad ta kasar ta Siriya ta nemi taimakon soja da makamai daga kasashen da suke kawance domin dakile abin da ta kira 'yan ta'adda da masu ba su taimako.