1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fata kan ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran

Matthias von Hein ATB
June 8, 2018

Shugaba Hassan Rouhani na Iran yana cikin mahalarta taron kolin kasashen kungiyar kawancen Shanghai inda yake fata kan tattauna batun ceton yarjejeniyar nukiliyar kasar da shugabannin China da Rasha.

https://p.dw.com/p/2zBO3
Hassan Rouhani
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Noroozi

Bayan batutuwan taron kolin kungiyar G7 ta kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya da aka fara yau Juma'a a Kanada, batun yarjejeniyar Iran zai kasance lamari bai sarkakiya  musamman barazanar takunkumin da Amirka ta yi na sanyaya gwiwa na kamfanoni daga bangarorin duniya tare da tara mai yawa ga duk wanda ya yi huldar kasuwanci da Iran.

Alamu dai sun nuna takunkumin zai yi tasiri a kan kamfanonin Turai da ke hulda a cikin Iran wadanda suka hada da kamfanin mai Total na Faransa da kamfanin motoci na Faransa wato PSA.

A waje guda dai manyan kasashe uku na Turai da suka hada da Jamus da Faransa da Birtaniya tare da kungiyar tarayyar Turai sun nuna adawarsu da yunkurin hana kamfanonin Turan yin hulda da Iran.

Putin und Jinping Konferenz CICA in Shanghai
Shugaba Vladimir Putin na Rasha (hagu) da Shugaba Xi Jinping na China (dama)Hoto: picture-alliance/dpa

Yayin da ake wannan dambarwa ta diflomasiyya, ganawar bayan fage da Shugaba Rouhani da zai yi da Shugaban Xi Jingping na China daura da taron kolin abu ne da ya dauka da matukar muhimmanci da kuma ganawa da Shugaba Vladimir Putin na Rasha.

Kawo yanzu dai babu daya daga cikin kasashen China da Rasha da ta amince da burin da Amirka take so ta cimma na shake makogwaron tattalin arzikin Iran domin kawo sauyin gwamnati a kasar.