1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran tayi barazanar janyewa daga yarjejeniyar hana yaduwar nukiliya

May 7, 2006
https://p.dw.com/p/BuzK

Majalisar dokokin kasar Iran,cikin wata wasika da ta aikewa sakatare janar na MDD Kofi Annan tayi barazanar tilasatawa gwamnati data janye daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta kasa da kasa,muddin dai kasar Amurka taci gaba da matsawa Iran din lamba ta dakatar inganta sinadarin uranium.

Wasikar wadda aka karanta a gidan rediyon kasar,tace ya kamata Kofi Annan da kuma komitin sulhu na majalisar dinkin duniya su magance matsalar nukiliya na Iran cikin ruwan sanyi,idan ba haka ba kuma,majalisar dokokin ta Iran bata da wani zabi sai dai ta bukaci gwamnatin kasar data janye daga wani bangare na yarjejeniyar wanda ya bada dama ga supetocin majalisar damar binciken tashoshin nukiliya na Iran,hakazalika sunce zasu sake duba sashe na 10 na yarjejeniyar wadda ya tanadi hanyoyin janyewa daga yarjejeniyar baki dayanta.