1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: 'yan kasarmu ba za su yi Hajji ba

Mouhamadou Awal BalarabeMay 12, 2016

KIka-kika da ke tsakanin gwamnatocin Saudiyya da Iran na neman hana dubban Musulmi da suka fito daga kasar ta Iran sauke farali a kasa mai tsarki a 2016.

https://p.dw.com/p/1In3s
Beginn Pilgerfahrt Hadsch in Mekka 01.10.2014
Hoto: Reuters/Muhammad Hamed

Gwamnatin Iran ta bayyana cewar 'yan kasarta ba za su sami damar sauke farali a kasa mai tsarki a bana ba, sakamakon rikicin da ake fama da shi tsakaninta da hukumomin Saudiyya.Ministan da ke kula da harkokin al'adu da addini na Iran Ali Jannati ne ya yi wannan sanarwa, inda ya ce ba a dauki matakan da suka kamata a kan kari ba. A cewar dai hukumomin na Saudiyya sun yi watsi da shawarwarin da Teheran ta yi basu a kan jigilar maniyata da basu viza.

Amma kuma a dazu-dazunnan Saudiyya ta karya zargin da aka yi mata na hana 'yan Iran zuwa aikin Hajji, ta na mai cewa Iran na neman bata mata suna ne.

Idan za a iya tunawa dai 'yan Iran 464 ne suka rasa rayukansu a turereniyar da ta salwantar da rayukan mahajjata 2000 a aikin hajji 2015.