Iran: Za a kare ofisoshin jakadanci
January 3, 2016
Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne dazu bayan da wasu masu zanga-zanga suka afkawa ofishin jakadancin Saudi Arabiya da ke Tehran tare da cinna masa wuta a wani mataki na nuna fushinsu kan kisan da Saudiyya din ta yi wa malamin Shi'ar nan Nimr al-Nimr a ranar Asabar.
A wasu sakonni da ya aike da su ta shafinsa na Twitter, Rouhani ya ce wannan danye aikin da aka yi na kone ofishin jakadancin Saudiyya din aiki ne na wasu mutane da ya ce sun wuce gona da iri, a hannu guda ya ce gwamnati za ta yi dukkanin mai yiwuwa wajen kare ofisoshin jakadancin kasashen duniya da ke kasar.
To sai dai a share guda ya sake jaddada matsayin gwamnatinsa na nuna rashin amincewarta da aiwatar da hukuncin kisa kan Nimr al-Nimr inda ya ce hakan ya saba wa dokokin addinin Islama sannan yin karen tsaye ne ga 'yancinsa a matsayinsa na dan Adam.