1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran za ta ci gaba da makamashin nukiliya

Abdullahi Tanko Bala
June 5, 2018

Kasar Iran ta sanar wa MDD kudirin bunkasa makamashinta na nukiliya bisa ka'idar yarjejeniyar da ta cimma da manyan kasashen duniya a 2015

https://p.dw.com/p/2yyll
Inspektion eines irakischen Atomkraftwerks
Hoto: AP

Iran ta sanar da hukumar makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya cewa za ta inganta makamashinta na nukiliya bisa ka'idar yarjejeniyar da ta cimma a 2015 da manyan kasashen duniya.

Gidan talabijin din kasar ya ruwaito Behrouz Kamalvandi mai magana da yawun hukumar makamashin nukiliyar ta Iran na cewa sun aike da takarda domin sanar da hukumar makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya kan batun.

Daraktan cibiyar makamashin nukiliyar Iran din kuma mataimakin shugaban kasar Ali Akbar Salehi ya tabbatar da cewa kasarsa ta fara aiki kan inganta rodikan makamashi a tashar Natanz.

Jagoran addini Ayatollah Ali Khameni a ranar litinin ya bada umarnin cigaba da aikin inganta makamashin yana mai alwashin cewa Iran za ta martaba kudirinta duk da ficewar Amirka daga yarjejeniyar da aka cimma a 2015.

Iran dai ta musanta zargin cewa tana yunkurin kera makamin kare dangi, inda ta ce shirinta na lumana ne domin samar da wutar lantarki.