1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran za ta ci gaba da shirin nukiliyarta

Ramatu Garba Baba MNA
September 22, 2017

Kasar Iran ta ce za ta ci gaba da kera makaman kare dangi ba tare da bukatar amincewar wata kasa ba.

https://p.dw.com/p/2kYUD
Iran Hassan Rohani
Hoto: Getty Images/AFP

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ce kasar ta kera wani makami mai cin dogon zango a yayin gudanar da wani kasaitaccen faretin sojoji don tunawa da rikicin yaki da ya auku a tsakanin kasar da kasar Iraki a shekarun 1980. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Amirka ke matsa kaimi na ganin Iran ta yi watsi da shirin nukiliyarta, inda take cewa kera makamai na kare dangi da kasar ke yi na da hadarin gaske.

Batun shirin nukuliyar Iran da Koriya ta Arewa su ne suka mamaye taron Majalisar Dinkin Duniya na bana. Shugabannin kasashen Amirka da Koriya ta Arewa sun yi ta musayar zafafan kalamai kan gwaje-gwajen makamai da Koriya ta Arewa ke ci gaba da yi. Sai dai a na shi bangaren ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bukaci bangarorin da ke tayar da jijiyoyin wuya da su kai zuciya nesa.