Iran za ta fuskanci tsauraran takunkumi
June 9, 2010Kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin ka'ɗa ƙuri'a akan ƙudurin sanyawa Iran tsauraran takunkumi. Ƙuri'ar, wadda ake sa ran ka'ɗata in anjima kaɗan, ta biyo bayan tsawon kwanaki biyun da mambobin kwamitin suka ɗauka ne suna tafka muhawara. Sakatariyar kula da harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta bayyana cewar, idan har aka amince da takunkumin, to kuwa shi ne zai kasance mafi tsaurin da Iran za ta fuskanta.
Takunkumin dai, zai haɗa da tsaurara bincike akan bankunan ƙasar Iran dake da ala'ƙa da shirin niukiliyar ƙasar, kana da sanya ido akan wasu manyan jami'an ƙasar da kuma kamfanonin dake da hannu wajen aiwatar da ayyukan niukiliyar ƙasar.
To, ahalin da ake ciki kuma Firaministan Rasha Vladmir Putin ya ce takunkumin da za'a sanyawa Iran ba zai yi wani ta'asiri ba, inda ya bada misali da ƙasar Koriya ta arewa wadda yace a yayin da al'ummomin ƙasa da ƙasa ke yin aiki da takunkumin da suka sanya mata, sai kwatsam hukumomin ƙasar suka sanar da cewar, sun mallaki makaman niukiliya. Akan haka ne Mr Putin, ya yi tambayar cewar, to, menene dalilin sanya irin wannan takunkumin kenan, tunda ba zai biya bukata ba?
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu