Iran ta ce a shirye ta ke ta tattaunawa kan batun Nukilliya
October 27, 2021Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian ya ce la'akari da tattaunawar da karamin ministan a harkokin wajen Iran ya yi da wakilan tarayyar Turai hakan na nuni da cewar za mu sake komawa tattaunawar, kana kuma kwanakwankin da ke tafe na sake bude tattaunawar ba sa da nisa.
Sai dai a bangarenta Kungiyar Tarayyar Turai ta ce ba wani abin da za ta iya fada a yanzu game da yunkurin sake komawa sulhun, ko da yake an ambato cewa ta yiwu EU ta sake tuntubar manyan kasashe duniya ciki har da Amirka game da yunkurinta na sake komawa kan teburin sulhu da Iran, bayan da gwamnatin Donald Trump ta yi fatali da yarjejeniyar a shekarar 2018. Ana sa ran farkon makon gobe ne za a tsayar da ranar da bangarorin biyu za su yi tozali dan cigaba da soma tattaunawar.