1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran za ta maka Amirka a kotun ICC

Yusuf BalaMay 10, 2016

Shugaba Hassan Rowhani ya fada wa kamfanin dillancin labaran ISNA, Iran ba za ta bari ba a kwace mata kadarori.

https://p.dw.com/p/1IlIY
Iran Politik Hassan Rohani
Shugaba Hassan RowhaniHoto: Mehr

Kasar Iran ta bayyana shirinta na maka Amirka a kotun kasa da kasa ta ICC da ke a birnin The Hague, wannan shiri dai na zuwa ne bayan da wata kotun koli ta Amirka a watan da ya gabata ta jaddada hukuncin karbe wasu kadarori mallakar Iran da biyan diyya ga wadanda harin ta'addanci da Iran ta dauki nauyin yinsa.

Shugaba Hassan Rowhani ya fada wa kamfanin dillancin labaran ISNA a ranar Talatan nan cewa kasar ta Iran ba za ta zura ido ba tacna kallon Amirka ta kwace mata wasu kadarorinta.

Wannan kotu dai a hukuncin da ta fitar ta bada dama ga wasu iyalai na Amirkawan da suka mutu a hare-haren su karbi diyya da ta kai Dala miliyan dubu biyu daga hannun gwamnatin kasar ta Iran.

Wadanda iyalansu za su ci moriyar wannan kudade dai su ne harin bama-bamai ya ritsa da su a barikin sojan kundunbalar Amirka a Beirut da wasu hare-hare da suka hadar da na rukunin gidajen yankin Khobar a Saudiyya a shekarar 1996.