Iran za ta taimaka wa Iraƙi da makamai
July 1, 2014Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian wanda ya sanar da hakan a birnin Moscow ya ce, Iraƙi tana da rundunarta mai ƙarfi, ko da shi ke ƙasarsa za ta aike da masu ba da shawarwari kan harkokin soji.
Kawo yanzu dai Iraƙi ba ta nemi irin wannan tallafi ba, amma a shirye suke wajen ba da makamai domin yaƙar ayyukan ta'addanci. Iran ɗin mai mafi yawan al'umma ' yan Shi'a ta lashi takobin goyon bayan Bagadaza wajen yaƙar mayaƙan jihadi na Sunni a ƙarƙashin jagorancin ISIS, waɗanda mayaƙansu suka mamaye yankuna biyar na Iraƙin da ƙaddamar da fafukar kafa ƙasar musulunci a watan Juni.
A wannan Talatar ce dai 'yan majalisar dokokin Iraƙin Ƙurdawa da Sunni, suka fice daga zaman sabuwar majalisar na farko, sakamakon gazawar Shi'awan wajen gabatar da sunan sabon Fraiminista da zai maye gurbin Nuri al-Maliki. Batu da ke dasa ayar tambaya dangane da shirin gaggauta kafa gwamnatin hadin kan ƙasa, da zai ceci Iraƙin da rugujewa.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdourahamane Hassane