Iran zata cimma burin bunkasa makamashinta nan da shekara guda
November 20, 2006Talla
Iran ta lashi takobin cigaba da bunkasa sinadran Uranium dinta ,domin cimma bukatun makamashin da kasar ke bukata cikin shekara guda,sabanin kiran da komitin sulhun mdd yayi wa kasar.Shugaba Mahmoud Ahmadinejad ya bayyana cewa nan da shekara mai zuwa,Iran zata cimma burinta na samarda makashin da take bukata.Iran mai arzikin man petur dai,tayi watsi da zargin da ake mata na kokarin kera bomb,dacewa tana samarwa kasar hasken wutan lantarki.Wannan jawabi na shugaba Ahmadinejad yazo ne adaidai lokacin da Amurka da kasashen turai ke kira ga hukumar kula da makamai ta mdd,datayi watsi da bukatun iran adangane da tallafin fasaha ,domin samarwa cibiyar nauranta da ake ginawa a Arak,dake kudancin Tehran kariya.