Iran zata gina sabbin tashoshin makamashin nukiliya
April 22, 2006Talla
Jakadan Iran a hukumar MDD mai sa ido a ayyukan nukiliya ta kasa da kasa, IAEA ya ce kasar sa ta kulla wani shirin hadin guiwa don samar da sinadarin uranium a cikin Rasha. To amma har yanzu ana nazari kan ka´idojin yarjejeniyar. Ali Asghar Sultani bai yi bayani ba ko shirin hadin guiwar sarrafa uranium din zai maye gurbin tace wannan sinadari da ake yi a cikin kasar ta Iran. Har yanzu dai hukumomin kasar sun dage cewa zasu bijirewa kiran da MDD ta yi kana kuma zasu ci-gaba da tace sinadarin uraniuma cikin kasar. Tun a cikin watan fabrairu ma Iran ta taba ba da sanarwar cimma irin wannan yarjejeniya da Rasha, amma ba´a samu wani ci-gaba ba saboda kin da gwamnatin Teheran ta yi na dakatar da shirin bunkasa uranium a cikin gida. A wani labarin kuma gwamnatin Islama ta Iran ta ce a cikin wata mai zuwa zata gaiyaci kamfanoni daga ko-ina cikin duniya don neman kwangilar gina wasu sabbin tashoshin samar da makamashin nukiliya guda biyu a cikin kasar.