1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Gangamin adawa da matakan Amirka

Yusuf Bala Nayaya
November 4, 2018

Gangamin na zama mai zafi sakamakon ficewar Amirka daga yarjejeniyar nukiliyar 2015 tsakanin Iran da kasashen yamma, abin da ya sa Amirka kara wa Iran takunkumi.

https://p.dw.com/p/37e0a
Iran Jahrestag Besetzung US-Botschaft Demonstrationen
Hoto: ILNA

Dubban al'ummar kasar ta Iran ne suka fita zanga-zangar, inda suka rika kira na ganin bayan Amirka. Wanda dai na zuwa ne yayin tunawa da kwace ofishin jakadancin Amirkan a Iran, a lokacin juyinjuya halin Musulunci na shekarar ta 1979, da kuma tuni da tarin takunkumin na Amirka kan albarkatun mai da kasar ke da su. 

Dalibai da dama da suka halarci wannan gangami da aka watsa shi kai tsaye ta kafar yada labaran kasar ta Iran, sun rika kona tutar Amirka da hotunan Shugaba Donald Trump. Dalibai ne dai 'yan gani kasheni a kasar ta Iran a rana mai kama ta yau hudu ga watan Nuwambar shekara ta 1979 suka afka wa ofishin jakadancin na Amirka a Iran, jim kadan bayan faduwar gwamnatin Shah da ke samun goyon bayan Amirkan, inda aka yi garkuwa da Amirkawa 52 tsawon kwanaki 444. Tun daga wancan lokaci kasashen biyu suka zama manyan abokan gabar juna.

Wasu rahotanni dai daga kafafan yada labaran cikin gida na cewa miliyoyin al'ummar ta Iran ne daga sassan kasar, suka fita wannan gangami inda a yayinsa suka rika nuna mubayi'arsu ga shugaban addini Ayatollah Ali Khamenei.