Irin kyautar da Jamusawa ke yi a lokacin bikin Kirsimeti
Euro 472 Euro: Yawan kudin da Bajamushe kan kashe kenan wajen sayen kyautukan Kirsimeti da suka hadar da littattafai na musamman, walau sabbi ko kuma tsoffi da makamantansu.
Ra'ayin mata da Maza
Bincike ya nunar da cewar kashi 40 na mata, ba su da matsalar samun kyautukan tsoffin abubuwa. Kaza lika kashi daya daga cikin uku na mazan sun nuna fahinta game da hakan. Sai dai kashi 11 daga cikin 100 ba su da ra'ayin sayen kyautukan Kirsimeti.
Ba dukkan kyautuka ba ne tsoffi
A wannan shekarar Jamusawa sun kashe a kalla Euro 472 a sayen kyautukan Kirsimeti, a cewar binciken kungungiyar kula da hada hadar kasuwanci da kasa. An samu karin wajen Euro bakwai fiye da shekara ta 2017. Ka na ya gaza da Euro biyar a kudin da aka kashe a shekara ta 2016. 'yan kasuwa na saran cinikin a Euro biliyan 100.
An fi bayar da kyautar katin kudi na shaguna
An fi darajawa kyautar katin zabi-abun-da-ka-ke-so a matsayin kyautar Kirsimeti. Kungiyar 'yan kasuwar ta ce a 2018, yawancin Jamusawa sun fi bayar da katin kudi da za ka iya zabar littattafai ko kayan kyalli da na zuwa dandalin wasanni da shiga cinima. Kuma ana saran kashe Euro miliyan guda da dubu 800 a matsayin kyautar Kirsimeti a wannan fanni kadai.
Wace kyauta ce mafi dacewa?
Akwai su! Duk mutun daya daga cikin ukun Jamusawa sun fi son kyautar tufafi da kayan wasan yara da 'yar tsana. Mutane suna la'akari da mahimmancin darajar irin kyautar da ka bai wa mutum. Kama daga kayan zaki da kayan wasannin motsa jiki da kayan wasan yara kayan kyali zura turaruka duk suna cikin wannan rukuni.
Ranar Juma'ar rangwamen kaya
Tun daga watan Nuwamba ake fara sayayyen kayan bukukuwan Kirsimeti. Kamar saura, su ma Jamusawa na amfani da karshen makon wajen sayayye ta yanar gizo. Su kan kashe wajen Euro biliyan daya da dubu 800 a a sayayyen na Black Friday.
Kyaututtukar da ake mayarwa
Bayan sayen kyautar ana kuma mayar wa. Bayan bukun Kirsimeti, sama da kashi 40 daga cikin 100 na kayayyakin da aka saya ta yanar gizo ne ake mayar wa. Bincike ya nunar da cewar wajen kashi 79 ne ke mayar da kayayyakin fiye da maza, wadanda kashi 21 daga cikin 100 ne kawai.
Bai kamata a samu kuskure ba: Kan alawar cakula din Kirsimeti
Gabanin bukin Kirsimeti na wannan shekara, alawar cakula kirar Santa Claus wajen miliyan 145 aka sarrafa a nan Jamus. Kashi biyu daga cikin uku na kasuwanninsu. Kuma tuni aka fara sarrafa na alawar cakula na Bunny don bukin Ester da ke tafe.