IS ta dauki alhakin kai hare-hare a Teheran
June 7, 2017Kungiyar IS ta dauki alhakin jerin hare-haren ta'addancin da aka kai a wannan Laraba a majalisar dokokin Iran da kuma a hubbaran marigayi Imam Khomeini da ke a birnin Teheran, da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 12 a yayin da wasu kimanin 30 suka ji rauni. A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin farfagandarta na Amaq kungiyar ta IS ta ce wasu mayakanta ne suka kai harin kunar bakin wake a wuraren biyu masu muhimmanci.
Wannan dai shi ne karo na farko da kungiyar IS ta dauki alhakin wani hari da aka kai a kasar ta Iran. Kamfanin dillancin labaran kasar ta Iran na ISNA ya ruwaito cewa ministan cikin gida Abdolreza Rahmani Fazli ya kira taron gaggawa na kwamitin tsaro na kasar a yayin da aka baza jami'an tsaro a ko ina a cikin birnin kana aka rufe tashoshin jiragen kasa.
Dama dai tun a watan Maris din da ya gabata kungiyar IS ta wallafa wani faifayin bidiyo wanda a ciki ta sanar da shirin harar kasar Iran domin a cewarta maido ta a jerin kasashe mabiya tafarkin Sunni da kuma zubar da jinin mabiya mazhabin Shi'a wanda akasarin al'umar kasar ta Iran ke a kai.