1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta dauki alhakin hannu a harin da ya hallaka mutum 63

Ramatu Garba Baba
August 18, 2019

Kungiyar IS, ta dauki alhakin kai harin birnin Kabul da ya lakume rayukan masu shagulgulan biki akalla 63 tare da raunata wasu fiye da dari a daren ranar Asabar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/3O5Ra
Afghanistan Kabul Anschlag auf Hochzeitsfeier
Hoto: AFP/W. Kohsar

Kungiyar ta wallafa a wani shafinta na yanar gizo, yadda ta aika da wata mata da aka yi wa damara da bama-bamai, dakin da jama'a ke shagalin bikin auren. Kafin jama'a su ankara, bama-baman sun tarwatse. Shugaban kasar Ashraf Ghani, ya yi tir da alla-wadai da harin, ya kuma baiyana takaici kan rashin shigar da bangaren gwamnati a tattaunawar sulhu da Amirka da kuma kungiyar Taliban ke yi da ya ce, wani babban nakassu ne ga shirin samar da dawamamiyar zaman lafiya a kasar.


Duk da cewa, IS ta yi kaurin suna a kai wa kasar hare-haren ta'addanci, wannan harin da ya rutsa da mata da yara kanana, ya girgiza kasar dama sauran kasashen duniya da ke yi wa kasar fatan samun zaman lafiya.