1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ba za ta kaiwa Iran hari ba

February 6, 2012

Shugaba Obama ya ce baya tsammanin Israila na shirin kai hari akan kasar Iran a game da shirinta na nukiliya.

https://p.dw.com/p/13xjI
President Barack Obama answers a reporter's question about the European debt deal as he meets with Czech Prime Minister Petr Necas, not shown, Thursday, Oct. 27, 2011, in the Oval Office of the White House in Washington. (Foto:Charles Dharapak/AP/dapd)
Shugaban Amirka Barack ObamaHoto: dapd

A halin da ake ciki dai yanzu shugabannin kasashen duniya na ƙara baiyana damuwa cewa Israila na iya kaiwa kasar Iran hari, matakin da ake gani ka iya haifar da gagarumin yaƙi da ma durƙushewar tattalin arzikin duniya baki ɗaya. A wata hira da 'yan Jarida Obama yace yana so ya tabbatarwa da dukkan abokan hulɗarsu cewa Amirka na haɗa hannu da Israila domin warware wannan taƙaddamar cikin ruwan sanyi musamman ta fuskar diplomasiyya. Shugaban na Amirka ya ƙi baiyana cewa ko Israila za ta tuntuɓi ƙasarsa kafin ta afkawa ƙasar ta Iran. Ya kuma ce baya tsammanin Iran na da niyyar ɗaukar fansa akan Amirka. Ita dai Iran ta sha nanata cewa shirin ta na nukiliya na lumana ne domin samar da wutar lantarki ga jama'arta.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh